Mutum sama da miliyan uku ne suka gudanar da aikin Umara a Masallacin Harami a watan Ramadana na bana.
Shafin Haramain Sharifain na mahukunta masallatan harami na birnin Makkah da Madina ne ya wallafa hakan ranar Litinin a shafinsa na Twitter.
- Ruftawar gadar jirgin kasa ta yi ajalin mutum 23 a Mexico
- Hatsari ya yi ajalin mutum shida a hanyar Sagamu
A bara ce Saudiyya ta ba da lamunin dawo da ibadar Umara kamar yadda aka saba yi a baya.
Sai dai an samu sauye-sauyen al’amura sakamakon bullar annobar cutar Coronavirus da ta dagula al’amura a duk wani kwararo da sako na duniya.
Miliyoyin Musulmi ne bisa al’ada ke zuwa ibdar Umarah duk watan Ramadan, inda a yanzu an samu ci gaba bayan sassauta dokokin dakile yaduwar cutar.
Alkaluman da mahukunta Saudiyya suka fitar sun nuna cewa mutum 6,979 cutar coronavirus ta kashe inda a halin yanzu an yi wa kimanin mutum miliyan rigakafin cutar.