Ma’aikatar Agaji da Kyautata Rayuwar Al’umma ta sanar da rufe rijistar neman aikin N-Power yayin da sama da mutum miliyan biyar ne suka nemi aikin.
Wata sanarwa da Ministar Agaji da kyautata rayuwa Sadiya Umar Farouk ta fitar na cewa mutum 5,042,001 ne ke neman a dauke su aikin wanda aka rufe wa’adin yin rijistar a ranar 9 ga watan Agusta 2020.
“Ma’aikatar ta tabbatar da cewa wadanda suka cancanta ne kawai za a fitar da sunayensu kuma za a tuntube su, sannan a wallafa sunayensu”, kamar yadda Ministar ta sanar.
Sadiya Farouk ta kara da cewa, za a bai wa mata da masu nakasa muhimmanci a guraben aikin.
A cewarta shirin N-Power an kirkiro shi ne don samar wa matasan Najeriya aiyukan yi, wanda hakan zai taimaka wa kasar daga farfadowa daga halin kuncin da jama’a suka samu kansu lokacin annobar COVID-19.
An dai fara rajistar ne a ranar 26 ga watan Yuni 2020 inda wa’adin zai kare ranar 26 ga watan Yuli 2020, amma daga bisani ma’aikatar ta kara wa’adin yin rijistar da mako biyu don wasu su samu damar yi.