Akalla mutum miliyan 7.4 ne za su jefa kuri’a a zaben Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Tarayya da ke gudana a Jamhuriyar Nihar ranar Lahadi.
Karon farko ke nan da wani zabebben Shugaban Kasar zai ta mika mulki ga magajinsa a Jamhuriyar Nijar, tun bayan samun ’yancin kasar.
Rahoton Jeune Afrique ya ce an samu jinkirin fara jefa kuri’a sai da misalin 9 na safe, a wasu yankuna na Niamey, babban birnin kasar.
Zabukan na gudana ne a yayin da kasar mafi fama da talauci a nahiyar Afirka (inji Majalisar Dinkin Duniya) ke fama da matsalar tsaro daga baga biyu:
Hare-haren mayakan Al-Qaeda da ISIS a Mali da Burkina Faso da ke Yamma da Nijar sun addabe ta; A Kudu maso Gabashinta kuma ayyukan mayakan Boko Haram daga Najeriya sun hana ta sakat.
An kashe mutum 4,000 a Burkina Faso, Mali da Najeriya a 2019 sakamakon rikice-rikice da ayyukan ’yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayin addini, inji Majalisar Dinkin Duniya.
Kalubalen sabon Shugaban Nijar
Gabanin zaben an kai munanan hare-hare biyu: mahara sun hallaka sojojin kasar bakwai a yankin Yammacin kasar a ranar 21 ga Disamba.
Kafin shi, Boko Haram ta kai harin da ya yi sanadin mutuwar fararen hula 34 a ranar 12 ga watan.
Duk wanda ya gaji Mahamadou Issoufou a shugabancin Jamhuriyar Nijar, yana kuma da jan aiki a gabansa a bagaren tattalin arzikin kasar.
Tuni dama sauin yanayi da faduwar farashin makamashin uranium da kasar ta fi dogaro da shi a kasuwanin duniya suka jefa tattalin arzikin kasar cikin wani kangi.
Uwa uba, ga tarnaki da kuma nakasun da annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arziki a ba ma a kasar ba kadai, har ma a duniya baki daya.
Alkaluman da Bankin Duniya na bara sun nuka 42% na ’yan Nijar na cikin fatara ta yadda suke rayuwa a kan Dala 1.90 a kullum; kashi 23% kuma sun dogara ne a kan abincin da kungiyoyin jinkai ke rabawa.
Ana hasashen dan takarar jam’iyya mai mulki kuma tsohon Ministan Harkokin Cikin Gida, Mohamed Bazoum na iya maye gurbin Mista Issuofou – wanda ke kammala wa’adinsa na biyu, kowannensu shekara biyar.
Mohamed Bazoum yana fafatawa ne da sauran ’yan takara 29, ga manya daga cikinsu:
Mohamed Bazoum
Ana hasashen Bazoum mai shekara 60 dan lele Shugaba zai iya kai bantensa a zaben na 2020.
Bazoum ya yi alkawarin ci gaba da ayyuka da manuforin Gwamnati Shugaba Issoufou na kawar da fatara da kuma yakar masu ta’addanci da sunan addini.
“Za mu dora a kan nasarorin da aka samu a shekara 10 da suka gabata,” kamar yadda ya fada a baya.
“Za mu ci gaba da abin da Shugaba Mahamadou Issoufou ya fara.”
Seini Oumarou
Seini Oumarou babban wakilin shugaban kasar ne tun shekarar 2016, amma yanzu ya sauka daga mukamin.
Karo na uku ke nan da jam’iyyar MNSD take tsayar da shi takara – 2011, 2016 da 2020 kuma jam’iyyar ce ta mulki kasar daga 1999 zuwa 20210.
Seini Oumarou mai shekara 70 shi ne tsoho Firaministan Nijar daga 2007 zuwa 2009.
Amadou Boubacar Cissé
Tsohon Minista a Ma’aikatar Tsare-tsare da Cigaban Kasa, Amadou Boubacar Cissé shi ne dan takarar jam’iyyar UDR Tabbat.
Mahamane Ousmane
Zababben Shugaban Nijar na farko a 1993, amma a 1996 sojoji karkashin tsohon Shugaban Mulkin Soja, Kanar Ibrahim Baré Mainassara suka hambarar da gwamnatinsa, saboda bore da aka samu a kasar.
Yanzu shi ne dan takarar jam’iyyar Renouveau Démocratique et Républicain.
Ibrahim Yacouba
Ibrahim Yacouba wanda ya zo na biyar a zaben Shugaban Kasar na 2016 da kashi 4.4 na kuri’un zaben da Shugaba Mahamadou Issoufou ya lashe.
Bayan ya kirayi magoya bayansa da su zabi Mista Issoufou a zagaye na biyun zaben, an nada shi Ministan Harkokin waje, amma aka sallame shi a 2018 bisa zargin “rashin ladabi”.
Yanzu Ibrahim Yacouba shi ne dan takarar jam’iyyar MPN.
Hama Amadou
A watan Nuwamba kotu ta yanke hukunci cewa tsayawa takarar Shugaban Kasa ta ”haramta” ga madugun ’yan adawa, Hama Amadou.
Kotun ba ta fadi dalilita ba, amma ana gannin hukuncin daurin shekara daya da aka yanke masa ne musabbabi.
A shekarar 2017 ne kotu ta yanke wa tsohon Firaminista kuma tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Kasar hukuncin daurin shekara daya saboda laifin ‘fataucin jarirai’.
A watan Maris na 2019 Shugaban Kasar ya yi masa afuwa, amma dokar zaben kasar ta haramta tsayawa takarar Shugaban Kasa ga duk wanda aka taba yanke wa hukuncin daurin akalla shekara daya a kurkuru.