✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum miliyan 50 na cikin kangin bauta da auren dole a duniya —MDD

An yi wa kusan mutum miliyan 25 auren dole, kuma akwai akalla mutum daya da ke cikin kangin bauta a cikin duk mutum 150 a…

Yawan mutane da ake yi wa auren dole ko suke shiga cikin kangin bauta a kullum ya haura miliyan 50 a fadin duniya.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa a cikin kowane mutum 150 a duniya, akwai akalla mutum daya da ke cikin irin wadannan nau’ikan kangin bauta na zamani.

Hukumar Kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya (ILO) ta bayyana a ranar Litinin cewa mutanen da hakan ta ritsa da su “ba sa su iya bijirewa ba ko barin auren saboda yaudara da barazana gami da azabtarwa da ake musu.”

Hukumar ta bayyana cewa binciken da suka gudanar ya gano fiye da rabin mutanen ana tursasa musu yin ayyuka na karfi da dangoginsu, rabi kuma, an yi musu auren dole.

Ta ci gaba da cewa adadin mutanen da ake wa auren dole da kuma bautarwa ya karu da kashi daya bisa biyar a shekarar 2022 da muke ciki.

Ta ce ta gano haka ne binciken da ta gudanar tare da Hukumar ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da hadin gwiwar gidauniyar Walk Free Foundation a karshen shekarar 2021.

Majalisar Dinkin Duniya dai na da muradin kawar da kowane nau’in bauta na zama zuwa shekarar 2030.

Sai dai ta ce yawan mutanen da aka gano suna cikin kangin bautar zamani da auren dole ya kauru da miliyan 10 daga shekarar 2016 zuwa 2021.

Lamarin ya kara muni ne bayan bullar cutar COVID-19, wadda ta jefa karin mutane cikin matsin rayuwa da karuwar basuka a kan jama’a.

Sauran dalilan sun hada da tashe-tashen hankula da kuma sauyin yanayi, wandan suka jefa mutane cikin matsanancin talauci da kuma gudun hijira.