Shirin Majalisar Dinkin Duniya na Samar da Abinci WFP, ya yi gargadin cewa akwai mutum miliyan 4.3 da za su yi fama da matsananciyar yunwa a wasu jihohi uku na Najeriya.
A cewar shirin na WFP (World Food Programme), jihohin uku sun hada da Adamawa da Borno da kuma Yobe da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar.
- Benzema ya shiga sahun ’yan wasa mafi zira kwallo a tarihin La Liga
- Zan ci gaba da biyan albashin ’yan sandan da aka kora daga aiki —Rarara
Shirin ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar, game da wani rahoto da ya tattara kan matsananciyar yunwa a yankin kasashen Kudu da Hamadar Sahara.
Shirin na WFP ya nuna damuwa kan rikicin da aka kwashe shekaru ana yi da ’yan bindiga zai iya jefa Najeriya cikin yunwa da tamowa.
Haka kuma, shirin ya ce wannan faruwa ne a yayin da miliyoyin mutane suka dogara kan taimako da ake ba su na abinci, wanda kuma suke fuskantar barazanar fadawa cikin yunwa.
“Kimanin mutum 600,000 na kan gabar fadawa cikin wannan musifa.
Mutane za su fuskanci yanayin neman daukin gaggawa saboda karancin abinci.
“Za kuma a fuskanci mummunar matsalar tamowa da mace-mace saboda karancin kai kayan agaji,” in ji shirin.