kasar Koriya ta Arewa ta bayyana cewa kimanin mutum miliyan uku da rabi da suka hada da ma’aikata da ’yan jam’iyya sun shiga sojin sa-kai a daidai lokacin da zaman tankiya a tsakanin kasar da Amurka ke ruruwa.
Jaridar gwamnatin kasar mai suna Rodong Simmun, ta ruwaito cewa dimbin mutanen da suka shiga sojin, sun yi haka ne, bayan da Kamfanin Dillancin Labarai na Tsakiyar Koriya (KCNA) ya fitar da wata sanarwa game da sababbin takunkumin da Majalisar dinkin Duniya ta kakaba wa kasar a ranar 7 ga Agusta.
Ana sa ran takunkumin da ya samu goyon bayan daukacin kasashe 15 da suke da kujerar naki a majalisar, ciki har da Amurka da Rasha da China, zai jawo rage kayayyakin da Koriyar ke fitarw zuwa kasashen waje da akalla rubu’i.
A tsawon makon jiya dai an rika musayar miyagun kalamai a tsakanin Shugaba Donald Trump na Amurka da gwamnatin Pyongyang bayan kakaba sababbin takunkumin, sakamakon gwaje-gwajen makamai masu linzami da Koriya ta rika yi.
Shugaba Donald Trump ya yi wa Koriya ta Arewa barazanar cikin fushi tare da aikewa da sakon tiwita da ke cewa “An kai Amurka bango.”
Wannan ya biyo bayan sanarwar da ke cewa Koriya ta Arewa tana da makamin nukiliya da zai iya kaiwa Amurka.
Gwamnatin Pyongyang a lokacin ta ce, tana duba yiwuwar kai wa Tsibirin Pacific na Amurka da ke yankin Guam.
An gudanar da wani jerin-gwano a manyan titunan birnin Pyongyang, hedlwatar Koriya ta Arewa a ranar 9 ga Agusta don nuna goyon baya ga gwamnatin Kim. Jerin gwanon wanda ya zo a daidai lokacin da zaman dar-dar ke dada ruruwa, nuna wa duniya ne irin karfin da Koroiyar ke da shi. Koriya ta Arewa dai ita ce kasar da ta fi kowace kasa yawan sojoji a duniya, inda yanzu haka take da sojoji miliyan daya da dubu 100 da kuma sojojin sa-kai da sauran masu aikin damara.