Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB), Dokta Akinwunmi Adesina, ya ce akalla mutum miliyan 283 ne suke kwana da yunwa a nahiyar Afirka.
Ya bayyana hakan ne a yayin tattaunawa da bayar da kyaututtuka kan abinci na duniya na Norman Borlaug na 2023 da ke Des Moines a Jihar Iowa da ke kasar Amurka a ranar Juma’a.
- Mutane miliyan 4.3 na fama da yunwa a Arewa maso Gabas – MDD
- Za a yi wa ’yan mata miliyan 7 rigakafin cutar kansar mahaifa a Najeriya
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, wanda shi ma yake halartar taron a wani bangare na bunkasa manufar Shugaban Kasa Bola Tinubu kan wadata kasa da abinci, ya gabatar da azuminsa a ranar Laraba.
Sai dai da yake gabatar da jawabinsa mai taken “Daga Dakar zuwa Moines”, Dokta Adesina ya ce sun ware Dalar Amurka biliyan ɗaya domin farfado da masana’antun sarrafa kayan gona a Jihohin Najeriya 24.
Ya ce za su gudanar da shirin ne da hadin gwiwar Bankin Raya Musulunci (IsDB) da Asusun Bunkasa Noma na Duniya (IFAD).
“Duk da ci gaban da aka samu a fannin aikin gona a Afirka, kusan mutum miliyan 283 har yanzu suna kwana da yunwa a Afirka.
“Wannan kusan kaso ɗaya ne cikin uku na yawan masu fama da yunwa miliyan 828 da ke fadin duniya,” in ji Adesina.