✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Mutum fiye da miliyan 7 na bukatar tallafi a Arewa maso Gabas’

Majalisar dinkin duniya ta bayyana ta bayyana cewa, akwai mutane fiye da miliyan 7 wadanda suke bukatar tallafi sakamakon rikicin Boko Haram a yankunan Arewa…

Majalisar dinkin duniya ta bayyana ta bayyana cewa, akwai mutane fiye da miliyan 7 wadanda suke bukatar tallafi sakamakon rikicin Boko Haram a yankunan Arewa maso Gabas a Najeriya.

Mutanen dake buqatar tallafin ‘yan jihohin Borno da Adamawa da Yobe ne.

Shugaban shirin UNDP Achim Steiner da shugaban bayar da agajin gaggawa na majalisar dinkin duniya Mark Lowcock ne suka sanar da hakan a yayin shirin mayar da ‘yan gudun hijira daga sansanoninsu zuwa gidajensu a kananan hukumomin Bama da Ngom da Mafa dake jihar Borno.