Hukumomi a Kasar Koriya ta Kudu sun fara bincike kan wasu mutum biyu da suka mutu bayan ’yan kwanaki da yi musu allurar rigakafin cutar coronavirus ta AstraZeneca.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa mutanen biyu da suka riga mu gidan gaskiya bayan karbar allurar rigakafin, suna fama da wasu cututtukan na daban.
- Dillalan Shanu da kayan abinci za su janye yajin aiki
- An kashe dan kasuwa bayan biyan fansar N5m a Sakkwato
Wata tsohuwa mai shekara 63 da ke jinya a gidan masu fama da cutar kansar jini, ta kamu da zazzabi mai zafi kwanaki hudu da yi ma ta rigakafin cutar a cewar Jeong Eun-kyeong.
Kamfanin Dillancin Labarai na Yonhap, ya ruwaito cewa a ranar Talata ne aka mayar da wani mutum zuwa wani Babban Asibiti bayan ya nuna alamun kamuwa da cutar gurbatar jini da kuma nimoniya.
Haka kuma, wani majinyaci mai kimanin shekara 50 da ke fama da ciwon zuciya da ciwon sukari, ya mutu a ranar Laraba sakamakon ta’azzara da ciwon zuciyar ya yi kwana daya da yi masa allurar rigakafin cutar Coronavirus ta AstraZeneca.
Sai dai kamfanin AstraZeneca ya ce yana sane da binciken da Hukumar Kula da Yaduwar Cututtuka ta Kasar Koriya ta Kudu KDCA ke yi a kan rigakafin.
Kamfanin ya ce an yi nazari da bincike mai zurfin gaske gabanin tabbatar da ingancin rigakafin ga lafiyar al’umma.
A yanzu haka KDCA ta bakin Darakta Jeong Eun-kyeong, ta ce mahukunta masu ruwa da tsaki na gudanar da bincike domin tabbatar da duk wata alaka da karbar rigakafin.
Da take zanatawa da manema labarai, Jeong ta ce a yayin da ake kirdadon sakamakon binciken gano duk wata alaka da karbar allurar, ta ce har kawo yanzu babu rai ko daya da ya salwanta a cikin mutanen da suka karbi rigakafin cutar Coronavirus ta kamfanin AstraZeneca ko Pfizer/BioNTech.
KDCA ta ce daga cikin mutanen da aka yi wa allurar, an samu mutum 207 da jikinsu bai karbi rigakafin ba inda suka rika nuna wasu alamu na rashin lafiya da a Turance ake kira anaphylaxis.
A makon jiya ne Koriya ta Kudu ta fara yi wa al’ummarta allurar rigakafin, inda ya zuwa daren ranar Talata aka yi wa mutum 85,904 sahun farko na rigakafin ta AstraZeneca yayin da kuma aka yi wa mutum 1,525 ta kamfanin Pfizer.
Alkaluman da Koriya ta Kudu ta fitar a ranar Talata sun nuna cewa an samu mutum 444 sabbin kamuwa da cutar doriya a kan jimillar mutum 90,816 da suka kamu a kasar baki daya.