Mutum biyu sun kone kurmus a bayan wata tankar fetur ta yi bindiga da talatainin daren Asabar a babban titin Ibadan-Legas.
Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Legas ta ce motar ta yi bindiga ne bayan ta yi hatsari daura da gadar Kara daga Legas, inda ta kona wasu motoci 28.
- Sai da na kusa zubar da hawaye ganin yadda aka yi wa Legas — El-Rufai
- Shaguben Jonathan bayan Biden ya yi wa Trump fintinkau
- Fitaccen mai yaki da ’yan fashi, Ali Kwara ya rasu
Kakakin hukumar na jihar, Olabisi Sonusi ya ce, “Tsananin konewar da mamatan suka yi ya sa ba za a iya gane ko su wane ne ba amma an gano cewa direban motar ne da yaron motar.
“Wasu ’yan daba dauke da muggan makamai sun hana jami’an ceto na FRSC da Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Legas isa wurin, amma daga baya jami’an namu sun isa wurin bayan jami’an tsaro sun isa wurin.
“Kwamandan Yanki, Olusegun Ogungbemide, da kansa ya jagoranci masu aikin ceto.
“Ana kokarin dauke motar kuma yanzu an bude hanyar amma jami’an FRSC na kula tafiyar ababen hawa suna shawartar ababen hawa da su sauya hanya”, inji shi.
FRSC ta kuma yi kira ga masu ababen hawa da su daure su rika kiyaye dokokin hanya a kowane lokaci.