✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum bakwai sun kone kurmus a hatsarin mota a Yobe

Hatsarin ya faru ne a kusa da garin Jakusko da ke Jihar

Wani hatsarin mota da ya auku a kusa da garin Jakusko da ke Jihar Yobe ranar Lahadi ya yi sanadin konewa tare da rasuwar mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama.

Rahotanni sun ce hatsarin ya faru ne tsakanin wata mota kirar Toyota Hiace mai cin mutum 18, wacce ta yi taho-mu-gama da wata karamar mota samfurin Honda da misalin karfe 10:00 na safe.

Wata majiya da ke kusa da inda abin ya faru ta shaida wa Aminiya cewar hatsarin ya faru ne yayin da motar Bus din da ta so daga garin Potiskum zuwa tana hanyar zuwa Gashuwa ta ci karo da Hondar, wacce ita kuma ta fito daga Gashuwa.

Majiyar ta ce nan take motocin biyu Suka kama da wuta suka kuma kone, lamarin da ya yi sanadiyar rasa ran mutum hudu a motar Bus din, uku kuma a karamar motar Hondar.

Kazalika, majiyar ta ce akasarin sauran fasinjojin motocin biyu sun tsira da munanan raunukan kunar wuta kuma suna can suka samun taimakon gaggawa a Babban Asibitin garin Jakusko.

Da yake bayani ga wakilinmu dangane da hatsari, Shugaban Karamar Hukumar Jakusko, Abdullahi Gwayo ya bayyana cewa, “Alal hakika wannan hatsari ya afku da a ranar Lahadi da wajen misalin karfe 10:00 na safe.

“Hakan ya jawo asarar rayukan mutum bakwai tare da samun raunukan akalla mutune bakwai.

“Sannan mun gano cewa hatsarin ya faru ne sakamakon fashewar tayar karamar motar, saboda a wajen da hatsarin ya faru babu rami ko kadan.”

Shugaban karamar hukumar ya kuma ce tuni Karamar Hukumarsa ta dauki nauyin kai wadanda suka samu raunukan Asibitin Gwamnatin Tarayya  (FMC) da ke Azare a Jihar Bauchi da kuma Asibitin Tarayya da ke Nguru (FMC) a Jihar ta Yobe, domin samun cikakkiyar kulawa.