Babban Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC), reshen Birnin Tarayya, Gora Wobin, ya ce mutane 994 sun rasu a hadura daban-daban a 2020.
Wobin ya bayyana hakan ne yayin tattaunawarsa da Kamfanin Dillacin Labarai NAN, a ranar Litinin.
- An cafke ‘yan Kano masu sayar da hotunan mata na batsa
- Sojoji sun yi juyin mulki a Myanmar, sun tsare Aung San Suu Kyi
- Najeriya ta rasa kwararren matukin jirgin ruwa a hadarin mota
“Idan aka duba yawan haduran da aka samu a 2020 da 2019, za a ga a 2020 ya sauka da kashi 14%.
“Daga cikin mutune 4,532 da suka yi hadari a 2020 mutane 201 ne suka rasu, a 2019 kuma mutane 248 ne suka rasu, an samu ragin kashi 18%.
“Mutum 1,728 kuma ne suka ji rauni a 2020, sabanin 2019 inda aka samu mutum 2,385.
“Mutane 2, 603 sun tsirage a haduran na 2020, yayin da a 2019 kuma 3,375 suka tsallake rijiya da baya,” cewar Wobin.
Ya bayyana cewa abubuwan da ke kawo hadura a Abuja sun hada da gudun da ya saba ka’ida, daukar kaya fiye da kima da sauransu.