Akalla mutum tare ne aka kama bisa zargin kashe Shugaban jam’iyyar APC na Jihar Nasarawa, Mista Phillip Tatari Shekwo.
Gwamnan jihar, Abullahi Sule ne ya bayyana hakan, yayin da yake karbar bakoncin kungiyar ‘yan kasuwa a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia.
- ‘A yanke min hukuncin rataya a bainar jama’
- An sace Shugaban APC na Jihar Nasarawa
- Buhari ya yi Allah-wadai da kisan shugaban APC na jihar Nasarawa
Kamar yadda ya bayyana “bayan kashe shugabanmu, hadin guiwar jami’an tsaro sun ci gaba da bibiyar lamarin.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa yanzu haka an cafke mutum 9, kuma ana bincikar su game da kisan shugaban namu.
“Muna kyautata zaron wadanda aka cafke din suna da hannu a kisan nasa domin su fuskanci hukuncin da ya dace da su”, cewar Sule.
Har wa yau, jami’an tsaro sun kashe mutum shida suka kuma kwato bingida kirar AK47 guda hudu a yayin binciken kisan shugaban na APC a Karamar Hukumar Loko.
Idan ba a manta ba marigayi Shekwo an yi garkuwa tare da kashe shi ne kwanaki shida da suka gabata.