Akalla mutum takwas ne suka rasa rayukansu a wani sabon hari da aka kai yankin Yelewta da ke Karamar Hukumar Guma a Jihar Binuwai.
Wani ganau ya shaida wa manema labarai cewar harin ya faru ne da misalin karfe 6 na yammacin ranar Talata, yayin da mutane ke kokarin tashi daga kasuwa.
- Sabon Harin Jos: An sa dokar hana fita ta sa’a 24
- Gwamnatin Jigawa ta tura dalibai 210 su karanci Likitanci a Sudan
Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP catherine Anene, ta tabbatar da faruwar harin inda ta ce mutum shida ne suka rasa rayukansu, sai dai ba ta yi wani karin bayani ba a kan hakan.
Shugaban Karamar Hukumar Guma, Caleb Aba ya ce ana zargin makiyaya ne suka kai harin gabanin lokacin da mutane ke kokrin tashi daga kasuwa.
“Ranar kasuwa ce kowa yana tsaka da hada-hada yayin da maharan suka kai hari.
“Sun rika harbe-harbe kan mai uwa da wabi wanda hakan ya yi ajalin mutum takwas sannan kuma ana zargin sun yi awon gaba da wani mutum da har yanzu ba a ganshi ba,” in ji shi.
Kazalika, Shugaban Karamar Hukumar ya ce an garzaya da wadanda suka ji rauni zuwa asibiti.
Ko da Aminiya ta tuntubi Sakataren Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN), Ibrahim Galma, ya ce ba shi da masaniya game da faruwar harin.
Sai dai wasu dakarun soji da ke sintiri a yankin da sun tabbatar da faruwar lamarin, inda wani daga cikinsu da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce an sake aiko da jami’ai yankin domin inganta tsaro.