✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 8 sun mutu a rikicin ’yan kungiyar asiri a Benuwai

Tsofaffi na mutuwa sakamakon karar harbe-harben bindiga da ya karade kauyen.

Wani rikicin ’yan kungiyoyin asiri ya salwantar da rayukan akalla mutum takwas a kauyen Onyagede da ke Karamar Hukumar Ohimini ta Jihar Benuwai.

Ganau sun ce kazamin fadan ya barke ne tsakanin kungiyoyin asirin Vikings da Black Axe tun da sanyin safiyar ranar Litinin, wanda ya ci gaba da faruwa har zuwa lokacin rubuta rahoton nan. 

Mazauna kauyen sun shaida wa Aminiya cewa ko baya ga wadannan mutum takwas da aka kashe, wadansu da dama sun samu raunuka yayin da mazauna suka tsere daga kauyen saboda tsoron harbin kan mai tsautsayi. 

Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ohimini, Kwamred Musa Alechenu, wanda ya tabbatar faruwar lamarin, ya yi kiran jami’an tsaro da su tabbatar da dawo da zaman lafiya a kauyen.

Ya kara da cewa tsofaffi na mutuwa sakamakon karar harbe-harben bindiga da ya karade kauyen. 

Ko da Aminiya ta tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Catherine Anene, bata amsa kiran wayarta ba, sai dai ta aiko sakon kar ta kwana cewa, “ba zan yi magana ba a yanzu.”