Rikicin kungiyoyin asiri ya yi ajalin akalla mutum 16 a Jihar Edo.
Dauki-ba-dadin ya auku ne a tsakanin mambobin kugiyar asiri ta Black Axe da kuma kungiyar Eiye Confraternity.
Aminiya ta gano cewa an faro rikicin na daukar fansa ne bayan wanda kungiyoyin biyu suka yi a ranar jajibirin Kirismeti.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa ’yan sanda sun kwashi gawarwaki akalla 16 a yankunan Okhoro, Medical Stores, Uwelu da Ebvaeke.
- Kano: Abba Gida-Gida ta sanya hannu kan kasafin 2024
- Soja ya kashe direban kayan agaji kan na-goro a Borno
Wani’yan sanda ta da ya ce ba a ba shi izinin magana a hukumance ba ya ce, “an kawo rahoto a caji ofis cewa an kashe mutum 16 a yankunan Esigie, Okhoro, Medical stores da kuma Uwelu da ke kananan hukumomin Oredo da Egor.”
Rikicin daukar fansan ya faro ne ranar 16 ga wata inda wasu ’yan kungiyar asiri suka kutsa unguwar Ogiso neman wani wanda suke zargin ya yi awon gaba da kudin da suka samu daga damfara ta inyane.
Amma da ba su gan shi ba, sai suka kashe mahaifiyarsa, lamarin da ya kai ga harin daukar fansa a ranar jajibirin Kirsimei inda aka kashe mutum hudu, ciki har da wani dan jarida.
Wakilinmu ya kira kakakin ’yan sandan Jiher Edo, SP. Chidi Nwabuzor, game da rikicin amma jam’in ya ce ba shi da labari.