✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 75 suka kamu da cutar amai da gudawa a Kudancin Kaduna

Kimanin mutane 75 ne aka bayyana sun kamu da cutar amai da gudawa a karamar Hukumar Jama’a da ke kudancin Jihar Kaduna a watan day…

Kimanin mutane 75 ne aka bayyana sun kamu da cutar amai da gudawa a karamar Hukumar Jama’a da ke kudancin Jihar Kaduna a watan day a gabata.

Daraktar Sashin Lafiya ta karamar Hukumar Jama’a, Uwargida Sarah Dadai ce ta bayyana haka a Larabar da ta gabata, a yayin da take jawabi ga ’yan jarida da sauran masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya a hedkwatar karamar hukumar da ke garin Kafanchan.

Ta ce bayan samuwar bayanin bullar cutar, an aika ma’aikatar lafiya ta jiha a Kaduna inda, su kuma ba su yi kasa a gwiwa ba, suka bayar da tallafin magunguna don shawo kan lamarin, kafin ya zama annoba.

Ta bayyana cewa kauyuka da unguwannin da suka hada da Tudun Wada da Katsit da Takau da Kafanchan ‘A’ da Goska da Garage, a matsayin wuraren da aka fi kamuwa da wannan ciwon, inda ta ce kananan yara ne daga wata hudu zuwa ’yan shekara daya zuwa biyu su ka fi kamuwa da ciwon. Sai dai babu wani rahoto na rasa rai da aka samu. Ta kuma bayyana cewa a cikin watan biyun da ake ciki, sau bakwai kawai suka samu rahoton bullar cutar.

A lokacin da yake nasa jawabin, Shugaban karamar Hukumar na Jama’a, Alhaji Yusuf Usman Mu’azu ya bayyana damuwarsa ga jama’ar da abin ya shafa kan samun jinkirin sanar musu da lamarin a kan lokaci sai dai ya yi alwashin shawo kan lamarin tare da bayar da duk irin tallafin da ake bukata tun daga kan wayar da kan mutane a lunguna da kauyuka har zuwa samar da kayayyakin gwaje-gwaje, inda ya umurci duk wani mai ruwa da tsaki a kan lamarin da su tashi haikan wajen sauke nauyin da ke kansu.