✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun mutu sakamakon fashewar tankar mai a Edo

Wuta tashi yayin da motar ta fadi a kasa.

Akalla mutum bakwai ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kauyen Agbede da ke Karamar Hukumar Etsako ta Yamma a Jihar Edo a ranar Lahadi.

An rawaito cewa hatsarin ya afku ne a kan babbar hanyar Benin zuwa Auchi, lokacin da wata tankar da ke jigilar man fetur ta bi ta kan wasu motoci, ta kashe mutum bakwai tare da jikkata wasu da dama.

Bayanai sun ce tankar ta zubar da man da ta dauko a kan titin yayin da ta kutsa cikin wasu motoci, nan take wuta ta tashi kuma ta kone wadanda ta rutsa da su.

Lamarin ya haifar da cunkoson ababen hawa a kan titin na tsawon sa’o’i kafin jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) su kai agaji wajen da lamarin ya afku.

Kwamandan Hukumar a Jihar Edo, Henry Benamaisa, ya tabbatar da faruwar hatsarin, inda ya alakanta lamarin da matsalar birki da motar dakon man ta samu.

Ya ce, “Motoci 14 ne hatsarin ya rutsa da su, da kuma mutum 25, wadanda bakwai daga cikinsu su suka mutu, wasu kuma suka samu raunuka daban-daban.

Kwamandan ya ce motar da ta nufi Auchi ta samu matsalar birki, wanda ana tsaka da haka wuta ta kama.

Ya ce an kai gawar wadanda suka mutu dakin ajiye gawa, wadanda suka jikkata kuma an garzaya da su asibiti don ba su kulawa.