✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun mutu bayan ruftawar rufin masallaci a Pakistan

Lamarin ya faru ne a yankin Ahmadpur da ke Gundumar Khairpur a Lardin Sindh.

Kimanin mutum bakwai ne suka mutu yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon ruftawar rufin wani masallaci a Kudancin Pakistan.

Kafafen yada labaran kasar suka ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Ahmadpur da ke Gundumar Khairpur a Lardin Sindh a sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi. 

Rahotannin sun bayyana cewa, sama da mutane 100 da suka hada da mata da kananan yara sun makale a karkashin baraguzan ginin masallacin.

Jami’an bayar da agaji gaggawa sun ce, mutanen da lamarin ya rutsa da su na barci a cikin masallacin a lokacin da lamarin ya faru.

Wadanda abin ya shafa dai galibi wadanda suka yi sansani ne a masallacin tun bayan da ambaliyar ruwan ta raba su da matsuganansu.

Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin a cikin kwanaki hudun da suka gabata ya haifar da hadurra da dama.