Kimanin mutum bakwai ne suka mutu yayin da wasu 10 suka jikkata sakamakon ruftawar rufin wani masallaci a Kudancin Pakistan.
Kafafen yada labaran kasar suka ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Ahmadpur da ke Gundumar Khairpur a Lardin Sindh a sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi.
- Buhari ba shi da alhakin magance matsalar tsaro —Isa Yuguda
- Kyandar Biri ta kara yaduwa a Najeriya — Kwararru
Rahotannin sun bayyana cewa, sama da mutane 100 da suka hada da mata da kananan yara sun makale a karkashin baraguzan ginin masallacin.
Jami’an bayar da agaji gaggawa sun ce, mutanen da lamarin ya rutsa da su na barci a cikin masallacin a lokacin da lamarin ya faru.
Wadanda abin ya shafa dai galibi wadanda suka yi sansani ne a masallacin tun bayan da ambaliyar ruwan ta raba su da matsuganansu.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yankin a cikin kwanaki hudun da suka gabata ya haifar da hadurra da dama.