✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 7 sun mutu, 53 sun jikkata a gobarar gidan caca a Thailand

Gobarar ta tashi cikin dare.

Wata gobara da ta tashi cikin dare a wani gidan caca ta yi ajalin akalla mutum bakwai, wasu takwas sun bace, a yayin da wasu 53 suka ji rauni.

Hukumomi a Kasar Thailand sun bayyana cewa gobarar ta tashi ne a gidan cacan da ke yankin Cambodia a kasar ne a ranar Laraba.

Har yanzu dai hukumomi ba su gano musabbabin tashin gobarar ba.

Hukumomin kasar sun ce zuwa yanzu mutum 32 aka yi wa magani daga cikin wadanda gobarar ta rutsa da su a lardin Sa Kaeo.

Jami’an tsaro da suka hadar da ’yan sanda, sojoji da ma’aikatan agaji ne suka yi wa gobarar taron dangi kafin daga bisani suka samu nasarar kashe wutar.

Kakakin Hukumar ’Yan Sandan Thailand, Chhay Kim Khoeun, ya ki yin karin haske kan adadin mutanen da suka jikkata.

Sai dai ya  bayyana cewa hukumomi na kokarin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su.

Gidajen caca na daga cikin wuraren yawon bude ido ga baki sannan yake kawo wa Thailand kudaden shiga.