✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 7 sun mutu, 5 sun jikkata a hatsarin mota a Neja

Hatsarin ya auku a daren ranar Talata.

Mutum bakwai sun rasu wasu biyar sun samu rauni a hatsarin mota a kauyen Gunu na Karamar Hukumar Munya a Jihar Neja.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) na jihar, Kumar Tsukwam, ya ce hatsarin ya faru a daren ranar Talata tsakain wata mota kirar Toyota Camry da wata bas.

“Hatsarin ya rutsa da mutum 12, amma mutum bakwai suka rasu,  biyar kuma sun jikkata.

“Mun samu kudi N36,200, buhun doya daya, kyamara kirar Nikon, katunan daurin aure, batirin waya guda biyu da kuma wata karamar jaka.

“Wadanda suka ji rauni an garzaya da su asibiti don ba su kulawa, wadanda kuma suka rasu an mika su dakin ajiye gawa na Babban Asibitin Minna.

“Ababen hawan da hatsarin ya rutsa da su an mika su caji ofis na Munya don gudanar da bincike,” in ji shi.

Tsukwam ya dora alhakin faruwar hatsarin kan gudun wuce ka’ida, sannan ya gargadi masu ababen hawa da su rika lura da irin gudun da suke yi a yayin tuki.