A ranar Talata 9 ga watan Yunin da muke ciki ne aka samu adadi mafi yawa na mutane da suka kamu da cutar COVID-19 a Najerirya a cikin awa 24.
Mutum 663 ne suka kamu da cutar a ranar daga jihohi 26, adadi mafi yawa tun farkon bullar cutar a watan Fabrairu.
Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta ce hakan ya kai yawan wadanda suka kamu da annobar 13,464 a kasar.
Alkaluman na zuwa ne yayin da hukumomin kasar ke kara sassauta dokar kullen da suka sanya domin dakile yaduwar cutar ta coronavirus.
- El-Rufai ya bude masallatan Juma’a, banda makarantu da kasuwanni
- ‘Coronavirus ta kashe mutum 587 a Kano cikin mako biyar’
- Masu coronavirus a Kano sun haura 1,000
Zuwa daren Talatar mutum 4,206 sun warke daga cutar wadda ta yi ajalin wasu 365 a jihohi 35 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
COVID-19 wadda kawo yanzu mutum 8,893 ke fama da ita a fadin kasar ta fi kamari ne a jihohi uku.
Jihar Legas ce ke kan gaba wurin yawan masu cutar ta COVID-19 da mutum 6,065, sai Kano da 1,020, sannan Abuja da mutum 1,012.
Daga ciki a Legas an sallami mutum 944 suka warke, 497 a Abuja da kuma 275 a Kano.