Harin da Isra’ila ta kai a tsakiyar Gaza ya kashe kimanin mutane 62 ciki har da mata da ƙananan yara, a cewar wasu majiyoyin kiwon lafiya a yankin Falasɗinu.
Dakarun tsaron Isra’ila (IDF) sun ce suna gudanar da bincike.
- Majalisar Dokokin Kaduna ta buƙaci a binciki El-Rufa’i
- Mai gida ya mutu yayin rikicin kudi da dan haya
Tun da farko dai, IDF ta ce ta fara kai hare-hare a al-Bureij da ke tsakiyar Gaza da kuma yankunan gabashin Deir al-Balah a ranar Talata.
Rundunar ta IDF ta kai hare-hare ta sama kan sansanonin soji da ma’ajiyar makaman Hamas, da kuma kayayyakin more rayuwa na ƙarƙashin ƙasa mallakar Ƙungiyar Islama ta Falasɗinu a Hamas.
“An kawar da ‘yan ta’addar Hamas da yawa a hare-haren da aka kai,” in ji IDF.
A baya dai an girke sojojin Isra’ila a al-Bureij a farkon wannan shekara, amma daga baya suka janye daga yankin.
Sai dai har yanzu Hamas na nan a yankin mai yawan jama’a, in ji IDF.
Mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke maƙwabtaka da al-Bureij da al-Maghazi sun sanar a ranar Laraba cewa an kai hare-hare ba tare da sassautawa ba a yankin.