Kimanin mutum 3,000 sun sun gudu daga muhallansu bayan harin ’yan bindigar da suka kashe mutum shida tare da sace darurwan shanu a Jihar Neja.
Rahotanni sun tabbatar cewa harin da aka kai a wasu kauyuka 12 na Karamar Hukumar Paikoro ta jihar ya kuma yi sanadiyyar jikkata mutum 20.
- ‘Yadda muke shiga kunci yayin zaman zawarci’
- Tsoron iyayenmu na hana maza neman aurenmu —’Yan matan barikin soja
- Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja
- ’Yan bindiga sun kashe shugaban karamar hukuma a Jihar Taraba
“’Yan bindigar suna da yawa, sun haura 200 kuma sun zo ne a kan babura.
“Sun wawure dukkannin kayan da ke cikin wani shagon sayar da sassan babura a kauyen Amale,” inji wani mazaunin yankin, Abubakar Azaido.
Ya ce “An fara kai harin ne da daren Asabar kuma sama da mutum 3,000 a yanzu haka sun gudu daga muhallansu,
“Ana ta zaman dar-dar da fargaba, mutane sai ihu suke ta yi suna guduwa kusan daga kowacce kusurwa.
“Maganar da nake maka yanzu haka, ina cikin babban asibitin Kaffin Koro inda muka garzaya da mutum 20 da suka ji raunuka.”
Abubakar ya ce ’yan bindigar sun kashe mutum hudu a kauyen Gwajau, biyu a Amale, sai kuma hudu da aka yi garkuwa da su a Dakolo tare da wani Fasto a kauyen Nani.
Sama da mutum 20 din da suka jikkata kuma suna babban asibitin garin Kaffin Koro ana kula da su.
Maharan sun kuma sace shanu fiye da 200 suka tafi da su kan iyakar jihohin Neja da Kaduna.
A cewarsa, garuruwan da aka kai wa harin sun hada da Amale da Beni da Barakwai da Kakuri da Gudani da Abolo da Nani da Gwajau da Kubi da Zakolo da Kado da kuma Dakolo.
Sai dai kokarinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Neja, Abiodun Wasiu ya ci tura zuwa lokacin hada wannan rahoton.