Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC), ta sanar da karin mutum 599 da aka samu sun harbu da cutar COVID-19 a ranar Talata.
Hukumar ta bayyana sabon adadin ne a shafinta na intanet a daren ranar Litinin.
- Daga Laraba: Yadda kuri’arku za ta iya sauya rayuwarku
- Rayuwar Zawarawa ’Yan Kannywood Sai Hakuri —Mansurah Isah
Daga cikin sabbin wadanda suka kamu Jihar Delta ce ke kan gaba da mutum 194, Edo na da 94, Abuja mutum 80, Kaduna mutum 48, sai kuma Jihar Legas mai mutum 35.
Ragowar jihohin sun hada da Ondo mai mutum 23, Kano na da 21, Ribas na da 20, Kwara 20, Ogun 18, Filato 12, sai Abiya da Kuros Riba kowannensu mutum takwas, Ekiti na da mutum shida, sai Jihar Bauchi mai mutum uku.
Yanzu dai adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan bullarta ya kai 239,019 sannan an sallami 213,180 da suka warke.
Yawan wadanda suka rasa rayukansu a sanadiyyar cutar kuwa ya kai 3,027
Tun a watan da ya gabata ne cutar COVID-19 ta sake kara yaduwa sabanin yadda a baya ta fara ja baya, kuma ta fara barazana musamman da samun bullar sabon nau’inta na Omicron.