Fararen hula 55 daga cikin wadanda kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a Jihar Borno sun tsere daga hannun mayakan kungiyar.
Mata 12 da kananan yara 27 da kuma maza 15 ne suka tsere daga hannun mayakan kungiyar da ke tsare da su a yankin Darajemel na Jihar Borno — Yanzu haka suna hannun sojoji.
- Tuwo ya yi ajalin mutum 9 ’yan gida daya a Zamfara
- Osinbajo zai halarci bikin mika sanda ga Sarkin Kano
Kakakin Hedikwatar Tsaro, Birgediya Benard Onyeuko ne ya sanar da haka ranar Alhamis, a bayaninsa kan ragargazar da sojoji suka yi wa ’yan Boko Haram da ISWAP ta kasa da kuma jiragen sama.
Birgediya Onyeuko ya ce ’yan Boko Haram da ISWAP akalla 73 ne sojoji suka aika lahira a cikin mako biyun da suka wuce a Jihar Borno.
Ya ce sojojin sun kwato bindigogi kirar AK 47 guda 44 da manyan bindigogin harbo jirgi guda bakwai da motocin da ake girke bindiga a kai guda bakwai da kuma PKT guda biyu.
Sauran sun hada da sinadaren hada abubuwan fashewa da kayan gyaran makamai da kayan abinci da motoci da barguna da sauransu.
Birgediya Onyeuko ya ce dakarun na Operation Hadin Kai da ke yaki da ISWAP da Boko Haram, sun yi wa sansanonin samun horo da maboyan kungiyoyin biyu ta sama da kasa a yankin Tabkin Chadi.
“Mun kai hare-hare kan sansanonin ’yan ta’addan da ke garuruwan Sabon Tumbu da Jibularam da kuma Kwalaram na Jihar Borno.
“Luguden bama-baman da muka yi sun tarwatsa sansanonin horaswar ’yan ta’addan a yankin Arewa-maso-Gabashin Jihar da kuma iyakokin Tabkin Chadi.
“Mun kai hare-haren ne bayan tattara bayanan sirri da suka nuna cewa wasu manyan kwamandojin ISWAP da Boko Haram na gudanar da taro a wuraren.
“Saboda haka muka tura jiragen yaki suka tarwatsa wuraren,” inji shi.