Hukumar Lafiya a kasar Ghana ta bayyana cewa sama da mutum 500 sun harbu da cutar coronavirus a wata masana’anta a kasar.
Ya zuwa yanzu wadanda suka harbu a kasar sun karu da kusan kashi 30 cikin 100 a cikin kwana daya.
Hukumar dai bata bayyana sunan masana’antar da aka samu hakan ba. A wani sako da ta fitar ta bayyana cewa a cikin ma’aikata dubu daya da 300 mutum 533 aka tabbatar sun harbu da cutar.
- COVID-19: A karo na biyu a jere, sabbin kamu sun haura 300
- ‘Yadda muka katange jihar Kogi daga COVID-19’
A ranar Alhamis, kasar ta Ghana ta rawaito jimillar mutum 4,012 wadanda suka harbu da cutar a fadin kasar, inda 18 suka rasa rayukansu.
Hakan dai ya sanya kasar Ghana take kan gaba a yawan wadanda suka harbu da cutar a Yammacin Afirka. Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ne a rawaito cewa kasar ta Ghana ita ce kuma kan gaba a yawan gwaje-gwaje da aka gudanar a yankin game da annobar.