Ana zargin mutum biyar sun mutu bayan fashewar wani abu da ake zargin bam ne a wurin shakawata a garin Leverkusen da ke kasar Jamus.
Sanarwar hakan ta fito daga bakin Shubaban Kamfanin Currenta, Frank Hyldmar yayin ganawarsa da manema labarai a ranar Laraba.
“Abin takaici ne domin ba lallai mutanen da suka bace a same su a raye ba, ” in ji shugaban Hyldmar.
Har wa yau, an tabbatar da mutum 31 sun ji rauni a sakamakon fashewar abun da ake zargin bam ne.
Sai dai bayanai sun ce ana zargin wanda suka rasa rayukansu a sanadiyar fashewar bam din ya kai mutum bakwai ya zuwa yanzu.
Hudu daga cikin wanda suka bace din ma’aikatan kamfanin Currenta ne, kamar yadda Hyldmar ya bayyana.
Kazalika, Hyldmar ya jajanta tare da mika sakon ta’aziya ga iyalan wanda lamarin ya rusta da su.