✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 5 sun mutu a fadan kabilanci ranar Kirsimeti a Delta

Kakakin 'yan sandan jihar, ya ce mutum biyu ne kacal suka rasa rayukansu.

Akalla mutum biyar ne aka ruwaito sun mutu sakamakon wani fadan kabilanci da ya kaure a tsakanin wasu matasan kabilar Ekpan a Karamar Hukumar Evwie ta Jihar Delta.

Aminiya ta gano lamarin ya faru ne a ranar bikin Kirsimeti, lamarin da ya sanya aka kai mutane da dama Babban Asibitin Garin Warri don yi musu magani.

Wata majiya ta ce “Fadan ya yi sanadin mutuwar mutum biyar na kabilar Ekpan cikin daren Asabar.

“Ba mu san abin da ya haddasa rikicin ba, amma an ce sakamakon fadan shugabanci ne daga bangarorin biyu.

“Tabbas harbin bindiga ne ya yi ajalin mutanen.

“Daya daga cikin wadanda abun ya rutsa da su dan kasuwa ne, wanda ya shafe tsawon daren yana murnar zuwan Kirsimeti.”

Da aka tuntubi Kakakin ’yan sandan Jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, sai dai ya ce mutum biyu ne kacal suka rasa rayukansu.