✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 5 sun jikkata a rikicin manoma da makiyaya a Jigawa

Tuni aka kai waɗanda suka ji rauni babban asibitin Dutse, domin yi musu magani.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa, ta tabbatar da jikkatar mutum biyar a wani rikici tsakanin manoma da makiyaya a dajin Hayin Kogi da ke ƙaramar hukumar Birnin Kudu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu ya fitar a ranar Litinin.

“Rahoton da muka samu ya nuna cewa, manoma da ke dajin Hayin Kogi sun farmaki manoma mazauna yankin Waza Fulani a ƙaramar hukumar Birnin Kudu lokacin da suke aikin gyaran gona.

“Sakamakon haka, wasu daga cikin manoman sun tsere su bar babur ɗinsu mai ƙafa uku, wayoyi da kayan aikin gonakinsu,” in ji shi.

Kakakin ya ƙara da cewa bayan samun rahoton, ‘yan sandan da ke yankin sun kewaye dajin.

Ya ce an kai wani mutum mai shekara 42 da kuma wasu huɗu da suka samu raunuka babban asibitin Dutse, domin yi musu magani.

“An ƙwato kayan manoman tare da ba su kayansu,” in ji Shiisu.

Ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda ake zargi da hannu a kai farmaki .

“Tun daga lokacin da lamarin ya faru kawo yanzu an samu zaman lafiya a yankin. Kwamishinan ‘yan sanda, Mista Ahmadu Abdullahi, ya bayar da umarnin cafke waɗanda ke da hannu a kai harin.

“Kwamisha ya bai wa kwamandan yankin Birnin Kudu da Kiyawa da ya gudanar da taro da masu ruwa da tsaki da nufin samar da zaman lafiya a yankin,” in ji shi.