✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rukunin farko na alhazan Kano sun tashi zuwa Saudiyya

maniyyata 505 daga Jihar Kano suka tashi zuwa kasar Saudiyya

A yau Litinin ne kimanin maniyyata 505 daga Jihar Kano suka tashi zuwa kasar Saudiyya don sauke farali a shirye shiryen da ake yi na Hajjin bana.

Maniyyatan wanda su ne rukunin farko sun tashi daga filin sauka da tashin jirage na Malam Aminu Kano da misalin karfe 11:30 na safe a cikin jirgin Max Air.

Ana sa rai maniyyatan za su sauka a Filin sauka da tashi na King Bn Abdulazeez da ke Jidda.

A jawabinsa na ban kwana, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi kira ga alhazan da su zama wakilai na gari ga jihar da ma kasar gaba daya, inda ya kuma yi kira gare su da su yi wa kasar addu’a don samun cikakken zaman lafiya da karuwar arziki.

Gwamnan ya kuma gargadi alhazan da su guji sanya kansu cikin harkokin tu’ammali da miyagun kwayoyi ko yin sata da sauran abubuwa marasa kyau don guje wa fuskantar hukunci mai tsanani daga kasar ta Saudiyya.

A jawabinsa tunda farko, Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Laminu Danbappa, ya bayyana cewa rukunin farko na alhazan sun fito daga ne kananan hukumomin Dala da Fagge da Gwale da Ungogo.

Dambappa ya yi kira ga alhazan da su kula da kudin guzurinsu tare da kashe su ta hanyar da ta dace.

Maniyyata 3,121 ne daga Jihar Kano ake sa rai za su sauke farali a bana