Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin kabilanci a Sudan ta Kudu ya kashe fararen hula 440 cikin watanni hudun karshe na 2021.
Rahoton da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a ranar Talata, ya nuna cewa rikicin da ya faru tsakanin wasu kabilu da ke rikici da juna a yankin Tambura cikin watan Yuni zuwa Satumba wanda ya hallaka daruruwan fararen hular.
- Ramadan: Sarkin Saudiyya zai ba ’yan Najeriya 12,600 abinci
- Yadda aka kama matashi da kullin Tabar Wiwi 39 a Kano
Rahoton ya dora alhakin rasa rayukan fararen hular kan mayakan da ke biyayya ga shugaba Salva Kiir da bangaren da ke adawa da su daga kabilar mataimakinsa, Riek Machar ne suka afkawa juna da taimakon daidaikun mayakan da suka assasa a yankin.
Kazalika, rahoton ya ce baya ga fararen hula 440 da suka mutu a rikicin akwai kuma wasu mutum 18 da suka jikkata kana wasu mutum 74 da aka yi garkuwa da su a tsakanin lokacin wata hudu.
Har wa yau, an bayyana cewa a tsawon lokacin, mata 64 sun fuskanci cin zarafi ta hanyar fyade ciki har da yarinya ‘yar shekara 13 wadda wasu tarin maza suka yiwa fyade har ta rasa ranta.
Sannan, rahoton ya ce har zuwa yanzu ana binciken wasu mutum 56 da suka bace, yayin da kuma mutum dubu 80 suka yi kaura daga mahallansu.