Ƙungiyar Shugabannin Kiristoci ta Kudancin Kaduna (SKCLA) ta yi tofin Allah tsine da kashe Rabaran Fada Sylɓester Okechukwu na Gundumar Katolika da ke Kafanchan, inda ta jingina haka ga taɓarɓarewar harkokin tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da Shugaban SKCLA, Dakta Emmanuel Nuhu Kure ya fitar a ranar Jumma’a ya miƙa ta’aziyyarsu ga Gundumar Katolika ta Kafanchan, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin.
- Fashewar tankar mai: Mutum 7 sun mutu, gonaki sun lalace a Neja
- An yi garkuwa da ɗan uwan Bishop Kukah da wasu 6 a Kaduna
“Wannan mummunar aiki babbar asara ce ga Coci da matuƙar tayar da hankali da damuwa game da ci gaba da kai hare-hare ga shugabannin Kiristoci a Kudancin Kaduna,” in ji Kure.
Inda ya koka da yawan kashe-kashen shugabannin addinin Kirista da suka yawaita, inda ya yi gargaɗin cewa ci gaba da kai wa malaman addini hari na iya ɗaukar wata ma’ana da ka iya rusa zaman lafiya a jihar. “Wataƙila ‘yan ta’adda masu aikata laifi ne ke aikata hakan, amma me ya sa ake kai wa ma’aikatan cocin hari su kaɗai?” inji shi.
SKCLA ta yi kira ga hukumomi da su tabbatar da anyi adalci ga malamin da aka kashe, tare da kiran mazauna yankin da su kasance masu sa ido game da abin da ya shafi tsaro sannan su riƙa sanar da hukumomi duk wani abu da ya bayyana musu.
Idan za a iya tunawa a ranar larabar da ta gabata ne wasu ‘yan bindiga su kayi sace Faston Katolika mai suna Rabaran Fada Sylɓester Okechukwu a yankin Tachira da ke ƙaramar hukumar Ƙaura ta Jihar Kaduna inda suka kashe shi ba tare da buƙatar komai ba.