Akalla mutum 44 ne suka mutu bayan wata ambaliyar ruwa da girgizar kasa sun shafe wani tsibiri dake gabashin kasar Indonesia da sanyin safiyar ranar Lahadi.
Iftila’in dai na zuwa ne ’yan sa’o’i kadan kafin mutane su tashi daga bacci domin fara bukukuwan Ista, inda wani ruwan sama mai kamar da bakin kwarya ya yi sanadiyyar ambaliya a tsibirin da mafi yawan mazaunansa mabiya darikar Katolika ne.
- Yadda aka yi bikin daukar gawar Fir’aunoni a Masar
- COVID-19: Mutum 7 sun mutu bayan karbar rigakafin AstraZeneca a Birtaniya
Gidaje da dama dai sun nitse a laka yayin da gadoji da yawa kuma suka karairaye
“Akwai mutum 44 da suka rasu, tara kuma suka sami raunuka a yankin, da yawa kuma yanzu haka na can sun nitse a cikin laka,” kamar yadda Hukumar Kula da Annoba ta Kasar ta shaidawa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP.
Masu aikin ceto dai na harsashen adadin wadanda suka mutun na iya karuwa a daidai lokacin da suke kokarin ci gaba da ceto mutane musamman a yankunan da lamarin ya fi kamari.
A wani labarin kuma, Hukumar Kula da Annoba ta Kasar ta ce wata ambaliyar ruwa a birnin Bima ta yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.
Madatsun ruwa a gundumomi hudu na kasar sun cika makil sannan suka batse, lamarin da ya yi sanadin shanye gidaje sama da 10,000 bayan an shafe sama da sa’o’i tara ana sheka ruwan sama ba tare da kakkautawa ba.
Munanan iftila’o’in girgizar kasa da ambaliyar ruwa ba bakin abubuwa ba ne musamman a lokacin damina a kasar Indonesia.
Ko a watan Janairun da ya gabata dai sai da akalla mutum 40 suka mutu sakamakon wata ambaliyar ruwan da aka yi a garin Sumedang dake yankin Java na yammacin kasar.
Masana muhalli dai na alakanta yawan sare bishiyoyi ba bisa ka’ida ba da cewa shi ke kara ta’azzara annobar.
Kasar dai ta yi harsashen cewa akalla mutum miliyan 125, kusan rabin adadin mutanen kasar ne ke zaune a yankunan da suke cikin barzanar fuskantar annobar.