Mutum 40 ne suka mutu, wasu da dama kuma sun jikkata bayan da wasu motocin bas guda biyu suka yi karo kusa da garin Kaffrine da ke Tsakiyar kasar Senegal a ranar Lahadi.
Shugaba Macky Sall ya ayyana makokin kwanaki uku daga ranar Litinin domin alhinin wadanda suka riga mu gidan gaskiya.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi ya kuma ce an samu mutuwar mutane 40 sannan kuma da dama sun samu munanan raunuka.
Shugaba Sall ya sha alwashin daukar mataki don hana aukuwar hakan a nan gaba.
A wata sanarwa da mai shigar da kara na Senegal ya fitar ya ce mutane 38 ne suka mutu da farko, inda aka samu karin mutum biyu daga bisani.
Mai gabatar da kara, Cheikh Dieng, ya ce binciken farko ya nuna cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wata motar bas dauke da fasinjoji ta kwace, biyo bayan fashewar wata tayar, kafin ta yi karo da wata motar bas kuma.
Kanal Cheikh Fall, babban jami’in Hukumar Kwana-Kwana ta kasar, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP cewa mutane 38 ne suka mutu yayin da 87 suka jikkata a hatsarin.
Babban jami’in ya ce wasu manyan motocin safa kirar bas biyu ne suka yi taho-mu-gama a wata babbar hanya da ke kusa da gari na Kaffrine.
A cewarsa, fasinjoji kimanin 125 ke cikin motocin biyu a lokacin aukuwar hadarin motar.
Wasu ‘yan kasar na zargin direbobin motocin haya da zabga gudun da ya wuce kima, lamarin da suke dangantawa da yawan haduran ababen hawa da ake samu a kasar.
Hatsarin dai ya kasance daya daga cikin munanan haduran mota da kasar ta fuskanta a shekarun baya-bayan nan.
A watan Oktoban shekarar 2020, akalla mutane 16 ne suka mutu, wasu 15 kuma suka jikkata, lokacin da wata motar bas ta yi karo da wata babbar motar dakon kaya a yammacin kasar Senegal.