Gobara ta yi ajalin Rabi’atu Bello, ’yar Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato, Bello Muhammad Sifawa, tare da ’ya’yanta uku da kuma ’yar aikinta.
Gobarar ta tashi ne a daren ranarLahadi a garin Sifawa da ke Ƙaramar Hukumar Bodinga a Jihar Sakkwato.
- An kashe N2trn kan gyaran lantarki amma kamar an shuka dusa
- Mutum 4 sun mutu, bankuna sun ƙone a gobarar tankar mai
Wutar ta kama gidan, inda ita da ’ya’yanta uku; namiji guda ɗaya da mata biyu suka rasa rayukansu.
Sai dai mijinta, Muhammad Bello Yusuf, wanda shi ne babban sakatare a ma’aikatar matasa ta jihar, ya tsira tare da wasu ’ya’yansu biyu maza.
Rabi’atu, ita ce babbar ’yar Sakataren Gwamnatin Jihar Sakkwato.
An jana’izarsu a ranar Litinin kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Yunƙurin jin ta bakin mahaifinta da mijin marigayiyar, ya ci tura saboda yanayi na alhini.