Hajiya Hauwa, mahaifiyar Sarkin Machina da ke Jihar Yobe, Alhaji Bashir Albishir Bukar Macina, ta rasu bayan ta sha fama da rashin lafiya.
A ranar Lahadi aka sallaci mahaifiyar sarkin mai suna Hajiya Hauwa Mai Bukar Machinawa a Fadar Sarkin Machina, da misalin karfe 11 na safe.
Daruruwan mutane ne suka taru domin halartar sallar jana’izar tata bayan Allah Ya yi mata cikawa a fadar dan nata.
Daya daga cikin jikokin marigayiyar, Bukar Adamu, ya bayyana cewar yadda jama’a suka yi tururuwar halartar jana’izarta ya nuna girman matsayin da suka dauke ta da shi.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’Yan Najeriya Suka Jure Wa Matsin 2024
- Yadda Saraki ya ci amanata a majalisa — Ndume
Ya yaba bisa yadda rayuwarta ta amfanar da al’umma yana mai yi mata addu’ar samun rahamar Allah, Ya kuma ba wa iyalan juriyar wannan babban rashi.
A sakon ta’aziyyarsa, Babban Sakataren Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Yobe, Dakta Kagu Abubakar, wanda shi ma jikan marigayiyar ne, ya ce “ita ce ta yaye ni daga hannun mahaifiyata, har akan ce wai ta sangarta ni a matsayin jikanta.
“Ta sanya mini lakabin Kwakori kuma ita na yi wa takwara da aka haifi ’yata ta fari, Hauwa.
“Mutuniyar kirki ce mai yawan alheri, Allah Ya gafarta mata, Ya sanya Aljanna Firdausi ce makomarta, Amin.“