Akalla mutum hudu sun rasu a gobarar da ta tashi a wata cibiyar kula da masu fama da cutar COVID-19.
’Yan sanda sun ce gobarar ta tashi ne a wani asibiti mai gado 30 a da ke wani bene a yankin a garin Nagpur na kasar Indiya a ranar Juma’a.
- Ba zafin kai kuka fi mu ba —Matawalle ga ’yan Kudu
- Magidanci zai shekara 400 a kurkuku saboda yi wa agolarsa fyade sau 900
- Sarkin Zazzau ya tumbuke rawanin Ciroman Zazzau
- Damfarar N450m: Kiristoci sun fi Musulmi tausayi —Ummi Zee-zee
A yayin aikin ceto, “An gano gawarwaki hudu a asibitin da ke hawa hudu na dan karamin ginin.
“An kuma dauke ragowar marasa lafiya 27 da aka kwantar a asibitin da ya yi gobara zuwa wani asibitin na daban,” inji wani Sufeton dan sanda, Sajid Ahmad.
Ba a kai ga gano abun da ya haddasa tashin gobarar ba, amma hukumomi sun ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike a kai.
A yankin na Nagpur da ke Jihar Maharashtra ne cutar COVID-19 ta fi yin kamari a kasar Indiya; Kashi 40% na mutum 145,000 da suka kamu da cutar a kasar na zaune ne a jihar.
Ana yawan samun gobara a kasar Indiya, yawanci saboda rashin, amfani da kayan hada wutar lantarki marasa inganci, tsoffin kayan da kuma rashin ingantattun hanyoyin kariya da na tsira idan wani abu na gaggawa ya faru.