✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 4 sun mutu a hatsarin mota a Kano

Hatsarin ya faru ne yayin da wani mai babur dauke da mutum uku ya yi kokarin wuce wata mota

Hatsarin mota ya yi sanadin rasa rayukan akalla mutum hudu, wasu da dama suka samu raunuka a kusa da kauyen Dinyar Madiga da ke Karamar Hukumar Takai a Jihar Kano.

Kakakin Hukumar Kashe Gobara na Jihar Kano, Saminu Yusif Abudullahi, ya ce lamarin ya faru ya yi da wani mai babur dauke da mutum uku ke yunkurin wuce wata motar safa.

Ya ce, “Da isa wurin da lamarin ya faru, jami’an kashe gobara sun gano wasu mutum hudu a sume, inda suka yi nasarar ceto wasu shida ciki har da direban bas din.

“Nan take an ba wa wadanda suka jikkata kulawa a kai asibitin NYSC na Takai, amma daga baya likitoci sun tabbatar da mutuwar mutum hudu,” in ji shi.

Kakakin hukumar, ya gargadi masu ababen hawa da su rika tabbatar da ki’yaye ka’idojin tuki domin kauce wa asarar rayuka da dukiyoyi.