Ma’aikatar Lafiya ta kasar Vietnam, ta ce mutum 122 sun rasu a kasar wasu sama da 325,604 sun kamu da zazzabin Dengue a bana.
Ma’aikatar ta ce adaddin wadanda suka kamu da zazzabin ya ninka kusan sau biyar idan aka kwatanta da na bara.
- Malami ya kashe abokinsa da shinkafar bera
- NAJERIYA A YAU: Yadda Dokar Rage Cire Kudi a POS Za Ta Shafi Zaben 2023
A cewar sashen yaki da cutar na ma’aikatar, mutum 269 ne suka harbu da cutar tsakanin watan Janairu da Nuwamba, yayin da biyar sun mutu.
Zazzabin Dengue nau’i dai zazzabin da cizon sauro ne ke haifarwa, kuma ne daya daga cikin cututtukan da ke yi wa lafiyar al’uma barazana.
Kazalika, sashen ya ce a bana an samu mutum 601 da suka ci abinci mai guba a fadin kasar, sannan 14 sun riga mu Gidan Gaskiya sakamakon hakan.
Har wa yau, sashen ya ce a halin da ake ciki, Vietnam na da masu dauke da kwayar cutar HIV 221,500, sannan 112,500 sun mutu sanadiyar cutar da ma sauran cututtuka masu nasaba da ita.