Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Ogun, Frank Mba, ya ce akalla mutum 30 ne rundunar ta kama bisa zarginsu da hannu a rikicin zabe da sayen kuri’u a zaben Gwamnan Jihar da aka kammala a ranar Asabar.
Mba, ya bayyana hakan ne ga manema labarai a ranar Alhamis yayin wata ziyara da ya kai ofishin Hukumar Zabe Ta Kasa (INEC) da ke Abeokuta, babban birnin Jihar.
- Babu wanda ya lashe zaben Shugaban Najeriya na 2023 – Mataimakin Peter Obi
- NAJERIYA A YAU: Ta ina Manhajojin hada-hadar kudi ta intanet ke samun kudadensu?
Ya ce, an kama wadanda ake zargin ne a sassa daban-daban na jihar bisa laifukan mallakar bindigogi ba bisa ka’ida ba, tayar da zaune tsaye da kuma sayen kuri’u a lokacin zaben.
Ya kara da cewar ‘yan sandan sun kuma kwato makamai da suka hada da bindiga da harsashi guda 25.
Kazalika, Kwamishinan ya ce an kuma kwato katin cire kudi guda 235 daga hannun wadanda ake zargin suna sayen kuri’u da su.
Mba ya ce, “An kama mutum 30 ne da laifuka daban-daban, tun daga mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, da kuma rashin da’a a rumfunan zabe, da aikata laifukan da ke iya haifar da rashin zaman lafiya da kuma laifukan da suka shafi sayen kuri’u.
“Mun kuma samu nasarar kwato bindigogi da harsashi 25.
“Har ila yau, mun kwato katin cire kudi na ATM guda 235 a hannun wadanda ake zargin.
“Ana ci gaba da gudanar da bincike kuma kamar yadda muka yi alkawari za mu tabbatar da doka da oda,” in ji shi.
Mba, ya bayar da tabbacin cewa za a mika wadanda ake zargin ga INEC domin a gurfanar da su a gaban kuliya bayan kammala bincike domin daukar matakin da ya dace da su.