Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta cafke wasu mutum uku kan yunkurin tada hargitsi da kuma satar kayan ‘yan magani a kasuwar Sabon Gari da ke jihar.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hussaini Gumel ne, ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN), a ranar Lahadi a jihar.
- Zanga-zangar kungiyar kwadago raini ne —Ministan Shari’a
- EFCC ta tsare masu sayar da sabbin takardun kudi a Kano
Gumel, ya ce lamarin ya faru ne daidai lokacin da wasu ’yan kasuwar ke kwashe kayayyakinsu zuwa sabuwar kasuwar Kano Economic City, da ke dangwauro, a wajen birnin.
Ya bayyana cewa wasu bata-gari sun yi yunkurin haifar da hargitsi a wurin, amma ba tare da bata lokaci ba ’yan sanda suka tarwatsa su.
A cewarsa, manufar wadanda ake zargin shi ne kutsawa cikin shagunan mutane domin satar kayayyaki.
Kwamishinan, ya ce wadanda ake zargin yanzu haka suna hannun ’yan sanda, inda ya kara da cewar sun bai wa ’yan kasuwar tsaro don kwashe kayansu cikin salama.
Ya ce an tura karin jami’an ’yan sanda kasuwar don bai wa ‘yan kasuwar damar kwashe kayansu cikin sauki da tsaro.
Idan ba a manta ba gwamnatin Kano, ta bayar da umarnin rufe shagunan masu sayar da magunguna a kasuwar Sabon Gari, lamarin da ya haifar da cece-kuce a jihar.
Wasu na ganin ba a yi ’yan maganin adalci ba.
A gefe guda kuwa, gwamnatin Kano ta bayyana cewar akasarin masu sayar da maganin da ke kasuwar ba sa kan ka’ida duba da dokokin da ke tattare da harkar sayar da magunguna.