Akalla mutum 26 ne suka saye kadarorin da gwamnati ta yi gwanjonsu bayan kwato su daga hannun barayin gwamnati.
Kadarorin sun hada da gidaje da filaye da aka kwato daga tsohuwar Ministar Man Fetur, Diezani Allison-Madueke, a Abuja da sauran wurare.
- Ambaliya: Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa wa Manoma 200 A Gombe
- An tura ’yan kwaya 3,500 cibiyar gyaran hali a Afghanistan
A shekarar da ta gabata Hukumar Yaki da Rashawa (EFCC) ta yi gwanjon kadarorin ga masu son sayen su.
A ranar Litinin hukumar ta fara mika kadarorin da aka saye na Legas da Abuja da Fatakwal da Kano da sauran wurare.
Sai dai kadarorin sun yi kwantai a ranar Liinin da aka yi gwanjon su, ko mutum guda ba a samu da ya sayi ko da daya daga cikinsu ba.
Amma mutum shida daga cikin 90 da suka nema suka yi nasara a rukuni na hudu a ranar Talata.
Da yake sanar da wadanda suka yi nasara a ranar Alhamis, mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce kadarori 26 sun samu shiga, 13 kuma sun gaza, saboda rashin cika ka’ida da sauransu.
A cewar Uwujaren, “Kadarori 39 ne a rukuni na biyar wadanda ke a wurare daban-daban a cikin Abuja.”
Ya ce za a sake bude kofa don bai wa mabukata su sayi kadarorin da suka rage a rukuni na biyar.
Da yake jawabi tun da farko, Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, wanda a gabansa komai ya gudana ya ce, hukumar ta yi aiki tare da masana harkokin gidaje don tabbatar da ba a sayar da wata kadara kasa da darajarta ba.
“Yadda muka tafiyar da tasarin haka lamarin yake a kasashen duniya.
“Muna da masana kadarori da suka tantance mana darajar kowace kadara, kuma muna sa ran sallama wa wanda ya biya fiye da saura.
“Saboda muna da bukatar tara wa Gwamnatin Tarayya kudi don aiwatar da sabbi da kammala wasu manyan ayyukan da ke gabanta a sassan kasa.
“Mun samu korafe-korafen jama’a kan dalilin rashin gudanar da shirin ta intanet. Mun jarraba haka, amma sai muka zabi tsarin da zai ba mu damar yin komai a bayyane don ’yan kasa su shaida,” in ji Bawa.
Daya daga cikin wadanda suka samu nasarar mai suna Chetanna Chukwudo, ya bayyana jin dadinsa tare da kira ga EFCC da ta ci gaba da kyakkyawan aikin da ta sa gaba saboda ’yan kasa na tsumayar kyakkyawan cigaba daga gare ta.