✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 26 sun fada a rijiya a wurin shagalin biki a Indiya

An ceto mutum 15 yayin da mutum 11 suka mutu nan take.

Akalla mata 26 da suka hada da manya da kananan yara sun fada a cikin wata rijiya a yayin wani shagalin biki a Arewacin kasar Indiya.

Lamarin da ya faru ne a daren ranar Laraba a kauyen Nebua Narangia a Jihar Uttar Pradesh, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 13.

Wadanda tsautsayin ya rutsa da su suna tsaye ne a kan wani karfe da aka rufe rijiyar da shi a lokacin wani bikin Haldi, daya daga cikin bukukuwan da ake gudanarwa a gidan ango.

Hukumomi a jihar sun bayyana cewa nauyin mutanen da ke kan karfe ne ya sa ya karye, wanda a nan take sama da mutum 20 suka fada cikin rijiyar.

Mutum 11 sun mutu nan take, yayin da kuma aka ceto mutum 15 amma biyu daga cikinsu sun rasu a asibiti.

Fira Ministan kasar, Narendra Modi, ya jajanta game da faruwar lamarin, inda ya ce gwamnatin kasar na kokarin tallafa wa wadanda abun ya rutsa da su.