Akalla mata 26 da suka hada da manya da kananan yara sun fada a cikin wata rijiya a yayin wani shagalin biki a Arewacin kasar Indiya.
Lamarin da ya faru ne a daren ranar Laraba a kauyen Nebua Narangia a Jihar Uttar Pradesh, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 13.
- Rikicin APC: Ganduje ya kayar da Shekarau a Kotun Daukaka Kara
- El-Rufai@62: Ayyukan El-Rufai abin koyi ne —Buhari
Wadanda tsautsayin ya rutsa da su suna tsaye ne a kan wani karfe da aka rufe rijiyar da shi a lokacin wani bikin Haldi, daya daga cikin bukukuwan da ake gudanarwa a gidan ango.
Hukumomi a jihar sun bayyana cewa nauyin mutanen da ke kan karfe ne ya sa ya karye, wanda a nan take sama da mutum 20 suka fada cikin rijiyar.
Mutum 11 sun mutu nan take, yayin da kuma aka ceto mutum 15 amma biyu daga cikinsu sun rasu a asibiti.
Fira Ministan kasar, Narendra Modi, ya jajanta game da faruwar lamarin, inda ya ce gwamnatin kasar na kokarin tallafa wa wadanda abun ya rutsa da su.