Akalla mutum 24 sun rasu bayan tashin gobara a wani asibitin kula da masu matsalar kwakwalwa a birnin Osaka na kasar Japan.
Hukumomin kasar sun fara gudanar da bincike kan gobarar ta ranar Juma’a, saboda zargin da gangan aka cinna wa cibiyar wuta.
- Tsohon Shugaban Shi’a ya koma addinin Hindu a Indiya
- An haramta yin dariya na tsawon kwana 11 a Koriya ta Arewa
Wani mai shago a kusa da wurin ya ce, “Na hangi wata yarinya a hawa na shida na benen tana ihu tana neman dauki, ban sani ba ashe akwai mutane da dama a ciki ginin; Wutar na da ban tsoro, babu abin da ta bari,” inji shi.
Dab da wayewar gari ne dai wutar ta fara ci a hawa na hudun ginin asibitin, wanda kuma ke kula duba sauran marasa lafiya.
Kafofin yada labaran kasar Japan sun nuna yadda bangaren ginin da ya kama da wuta ya kone kurmus a gobarar da suka ce mutum 24 sun mutu.
Kawo yanzu dai ’yan sanda ba su tabbatar da adadin mamatan da kafar yada labaran kasar, NHK, ta sanar ba.
Tun da farko dai hukumar kashe gobara ta kasar Japan ce ana fargabar lamarin ya ritsa da rayukan mutum 27.
Sai dai a kasar Japan, likitoci ne kadai ke sanar da mutuwa.