✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 23 sun bace bayan nutsewar jirgin ruwa a Kambodiya

’Yan kasar China 23 sun bace bayan jirgin ruwan fasinja dauke da mutum 41 ya yi hatsari a kasar Kambodiya.

Mutum 23 sun bace bayan wanin jirgin ruwan fasinja dauke da mutum 41 ya yi hatsari a kasar Kambodiya.

Ibtila’in ya auku da jirgin ruwan, wanda ke dauke da fasinjoji ’yan kasar China ne a yankin Sihanoukville na Kambodiya.

Kakakin yankin Sihanoukville, Preah Sihanouk, ya ce, “muna neman mutum 23 daga cikin fasinjojin da har yanzu ba a gani ba”.

Hukumomin kasar sun sanar a safiyar Juma’a cewa an yi nasarar ceto mutum 18 bayan aukuwar lamarin ranar Alhamis.

Preah Sihanouk, ya ce suna yi wa wadanda aka ceto din tambayoyi a yayin da ake ci gaba da aikin ceto, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

Kauyen Sihanoukville wanda a baya ya shahara da sana’ar kamun kifi, a baya-bayan nan ya zama wurin da ’yan China ke yawan zuwa yin kasuwanci.Sai dai rahotanni sun nuna ana amfani da kauyen — wanda yanzu ke samun yawaitar gidajen caca, — a matsayin hanyar safarar kauyawa ’yan kasar China zuwa birane ta haramtacciyar hanya.Shugaban ’yan sandan lardin, Chuon Narin, ya ce an gano fasinjojin jirgin sun baro tashar jiragen ruwa ta Guangdong da ke China ne a cikin jiragen ruwa masu gudu tun ranar 11 ga watan Satumba.Bayan kimanin mako daya, sai aka mayar da su wani jirgin katako, wanda wasu ’yan Kambodiya biyu ke tukawa.A ranar Alhamis kuma jirgin katakon ya fara nutsewa da su bayan ya tsage a cikin teku.

Dan sandan ya ce ana cikin haka ne wani kwalekwalen kamun kifi ya zo ya tafi da matukan jirgin ya bar fasinjojin.

Amma ya ce an kama matukan jirgin kuma ana bincikar su.