Mutum 23 sun bace bayan wanin jirgin ruwan fasinja dauke da mutum 41 ya yi hatsari a kasar Kambodiya.
Ibtila’in ya auku da jirgin ruwan, wanda ke dauke da fasinjoji ’yan kasar China ne a yankin Sihanoukville na Kambodiya.
- Masu hannayen jari a Najeriya sun yi asarar biliyan N124 ranar Alhamis
- NAJERIYA A YAU: Halin da ’yan gudun hijirar Bama ke ciki bayan komawa garinsu
- ASUU: Daliba ta bukaci kotu ta dakatar da albashin Buhari da na Gwamnoni
Kakakin yankin Sihanoukville, Preah Sihanouk, ya ce, “muna neman mutum 23 daga cikin fasinjojin da har yanzu ba a gani ba”.
Hukumomin kasar sun sanar a safiyar Juma’a cewa an yi nasarar ceto mutum 18 bayan aukuwar lamarin ranar Alhamis.
Preah Sihanouk, ya ce suna yi wa wadanda aka ceto din tambayoyi a yayin da ake ci gaba da aikin ceto, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Dan sandan ya ce ana cikin haka ne wani kwalekwalen kamun kifi ya zo ya tafi da matukan jirgin ya bar fasinjojin.
Amma ya ce an kama matukan jirgin kuma ana bincikar su.