Akalla fasinjoji 22 ne suka kone kurmus a wani hatsarin mota da ya auku tsakanin wata bas da tirela a yammacin kasar Jamhuriyar Benin.
Wata sanarwa da hukumomin kasar suka fitar, ta ce hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi a yankin Dassa-Zoume, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 22 tare da jikkata wasu da dama.
- NAJERIYA A YAU: Irin Tarbar Da Kanawa Suka Yi Wa Buhari
- Za a kai Murja Ibrahim gwajin kwakwalwa don gano ko tana da tabin hankali
Motar na makare da fasinjoji 40, mallakin kamfanin sufuri na Baobab da ta taso daga yankin Parakou zuwa Kwatano.
Da yawa daga cikin fasinjojin sun rasu bayan da motar ta kama da wuta.
Tuni kamfanin zirga-zirga motoci na Baobab, ya fitar da sanarwar dakatar da ayyukansa don gudanar da bincike da kuma taimaka wa iyalan wadanda suka mutu wajen gano gawarwarkinsu.